ADABIN QAURA: Tsokaci A Kan Wasu Waqoqin Baka Na Hausa A Qasar Libiya

Main Article Content

Kassim Mahanuod Bilal

Abstract

Wannan takarda mai taken, “Hjirar Adabi: Tsakaci a kan Wasu Waqoqin Baka na Hausa a Qasar Libiya,” wani yunquri ne na fito da yadda adabin wata al’umma yake yin hijira daga wata  qasa zuwa wata. A cikin takardar, an yi tsokaci a kan yadda maza da matasan wata al’ummar Hausawa da ke qasar Libiya suke rera waqoqin Hausa, waxanda kuma suke bayyana irin halayen rayuwarsu. An yi amfani da ra’in bincike na Nazarin Qwaqqwafi wanda aka xora shi a kan waqoqin don a yi tsokaci kuma a fito da irin saqonnin da waqoqin suke xauke da su, ta hanyar yin fashin baqin wasu muhimman kalmomin da ke cikinsu. An lura da yawancin waqoqin suna da sigar na baka na  yara masu amshin “iyee rayee diidee,” waxanda ‘yan mata ko samari ke rerawa a wasan dandali ko lokacin bukukuwansu. Haka kuma, ana amfani da kayan kixa ne da amshinsu ta fuskoki guda biyu. Akwai waxansu da ake rerawa da jagora da ‘yan amshi. Akwai kuma waxansu da ake rerawa tare, gaba xaya.

Downloads

Download data is not yet available.

Article Details

How to Cite
Kassim Mahanuod Bilal. (2020). ADABIN QAURA: Tsokaci A Kan Wasu Waqoqin Baka Na Hausa A Qasar Libiya. Journal of Human Sciences, 19(1), 110–115. https://doi.org/10.51984/johs.v19i1.935
Section
Articles