ADABIN QAURA: Tsokaci A Kan Wasu Waqoqin Baka Na Hausa A Qasar Libiya
Main Article Content
Abstract
Wannan takarda mai taken, “Hjirar Adabi: Tsakaci a kan Wasu Waqoqin Baka na Hausa a Qasar Libiya,” wani yunquri ne na fito da yadda adabin wata al’umma yake yin hijira daga wata qasa zuwa wata. A cikin takardar, an yi tsokaci a kan yadda maza da matasan wata al’ummar Hausawa da ke qasar Libiya suke rera waqoqin Hausa, waxanda kuma suke bayyana irin halayen rayuwarsu. An yi amfani da ra’in bincike na Nazarin Qwaqqwafi wanda aka xora shi a kan waqoqin don a yi tsokaci kuma a fito da irin saqonnin da waqoqin suke xauke da su, ta hanyar yin fashin baqin wasu muhimman kalmomin da ke cikinsu. An lura da yawancin waqoqin suna da sigar na baka na yara masu amshin “iyee rayee diidee,” waxanda ‘yan mata ko samari ke rerawa a wasan dandali ko lokacin bukukuwansu. Haka kuma, ana amfani da kayan kixa ne da amshinsu ta fuskoki guda biyu. Akwai waxansu da ake rerawa da jagora da ‘yan amshi. Akwai kuma waxansu da ake rerawa tare, gaba xaya.
Downloads
Article Details
Plagiarism policy
Sebha University Journal respects intellectual property and aims to protect the original work of authors applying for publication. In general, the laws of the magazine are inconsistent with scientific articles that contain stolen materials and are not bound by the standards of quality, research and innovation. Applicants for publication to the journal must adhere to ethical standards and refrain from plagiarism in any way. In the event that any plagiarism or scientific theft of an article submitted for publication is found, the journal will contact the author to provide their interpretation within two weeks of its date, after which it will be referred to the relevant committees formed for this purpose to take strict measures. about that. In general, the journal’s license allows the citation of the content published on its website and the download of all files.