Kimiyya da Fasaha: Nazarin Wasu Zantukan Hikima . Da Fasaha Na Hausa
Main Article Content
Abstract
Wannan Takarda mai suna: ( Kimiya Da Fasaha: Nazarin Zantukan Hikima Da Fasaha Na Hausa), Bincike ne da aka gudanar da shi a kan wasu zantukan hikima da fasaha na Hausa don kwatanta su da wasu fannonin ilimin kimiya da fasaha domin ganowa da kuma tabbatar da alaqar da ke tsakanisu. Binciken ya yi amfani da xakunan karatu da kuma saurare ta la’akari da ire-iren zantukan hikima da kuma fasaha na al’ummar Hausawa da kuma rubutawa da xaukar wasu a na’urar sadarwa ta hannu (handset/cellular phone). Sannan kuma an yi amfani da Ra’in Amfani da tunani/hankali wajen gano manufar al’amari na Lakoff da Johnson (1980) don tsettsefe abubuwan da aka samo domin samun inganci a wajen tabbatar da sakamakon binciken. Don haka, Binciken ya kawo wasu zantukan hikima da kuma fasaha na Hausa masu burbushin ilimin kimiya a cikinsu. Sannan kuma an yi bayanin yadda zantukan hikima da fasahar na Hausa suke xauke da ma’anoni guda biyu wato (1) ma’ana ta zahiri (literal meaning) da kuma (2) ma’ana ta baxini/adon harshe (figurative meaning). Haka kuma, an kawo ma’anar ilimin kimiya da kuma manyan fannonin da ilimin kimiya ya tattare. A qarshe, Binciken ya gano kuma ya tabbatar da samun vurvushin alaqa mai qarfi tsakanin wasu fannonin Ilimin Kimiya da Fasaha da kuma wasu zantukan hikima da fasaha na Hausa. Sannan kuma, an ba da shawarwari da kuma hasashen abubuwan da za su iya taimaka wa xalibai da kuma masu nazari wajen bunaqasa wannan harshen na Hausa da kuma kyautatata rayuwarsu da ta al’ummar qasarsu ta fannoni daban-daban, musamman ma ta vangaren wannan fannin na Kimiya da Fasaha.
Downloads
Article Details
Plagiarism policy
Sebha University Journal respects intellectual property and aims to protect the original work of authors applying for publication. In general, the laws of the magazine are inconsistent with scientific articles that contain stolen materials and are not bound by the standards of quality, research and innovation. Applicants for publication to the journal must adhere to ethical standards and refrain from plagiarism in any way. In the event that any plagiarism or scientific theft of an article submitted for publication is found, the journal will contact the author to provide their interpretation within two weeks of its date, after which it will be referred to the relevant committees formed for this purpose to take strict measures. about that. In general, the journal’s license allows the citation of the content published on its website and the download of all files.